Tarihin makarantar Active School da zantutuka masu sauki na me makarantar.


A shekara ta 2000, bayan shekaru da dama da karantar wa ne, ya

Waye mini cewa, in bude makarantar book da zai taimaka wurin ilimantar da dimbin jama’a, da sake ma yawanci rayuwan su, da kuma taimaka musu wurin sanin wasu mutane, al’adun su na gargajiya da kuma bude musu sabbin hanyoyin samun sa’a. Manufar makarantar book din nan itace, domin jama’a su samu Karin ilimi da zai taimaka wa rayuwan su, ta ci gaba a fannoni iri na (kasuwanci, kiwon lahiya, da kuma shugabanci). A shekaru nan gaba, makarantar zata fadada girman ta a duk fadin kasar, da kuma samun suna a duk fadin duniya. Matakai da dama da aka dauka wurin kafa makarantar itace, domin taimaka wa duniya baki daya, inda jama’a daga kasashe dabban dabban zasu hadu, su kawo ra’ayoyin su, su koyar a kuma koya musu, su karu a kuma karu da su.

Ina da yardan cewa, ko wani bil’adam na da nashi basira, yana kuma da wani abu da wasu basu da shi, hakan zai taimaka wurin kara musu ilimi. Kada ka rena wani a duniyan nan da muke ciki. Kada ka ga cewa kafi wani sani. Ka baiwa mutane daman Magana, kai ma ka saurare su. A lokacin da suke Magana, ka saurare su domin Karin ilimi da kuma samun basiran dake a cikin maganan su. Ka lura da irin abutan da kake yi. Idan kana abuta da mai basira, ka lura da abinda yasa yake da basira da abinda ya sa ya zama jarumi. Kowani mutun, an haife shi ne da nashi gwaninta iri dabban dabban. Manufar makarantar book din itace, sanin wayanan gwanintan domin amfani da su ta hanyar da ta kamata. Makarntar Active, gida ce ga duk mai neman taimako, kuma har matukan akwai ababan taimaka wa, zamu kai gare su daya bayan daya. A lokacin da muke koyar wa, da kuma yada ilimi a harsuna dabban dabban ga bil’adam, ya kamata a gane cewa, mabudin nasara shine kokari da himma a duk abu mai kyau da zaka yi wa rayuwan ka. Rayuwa bada ilimi ba, kamar miya ne da babu gishiri a cikin ta. Mutun da baya da ilimi, kamar soja ne da bai koyi aikin soja ba. Idan yaki ya tashi, shine farko mai gudu daga filin yaki. Yana da muhimmanci cewa, har dai kana da rai, ya kamata ka nemi Karin ilimi, domin ilimi kamar yanda muka sani shi a gishirn zamna duniya. Ilimi na sa kayi amfani da basiran da kake da shi. Akwai dimbin jama’a Allah ya ba basira, to amma basu samu cin albarkan basiran da Allah ya basu ba, domin kuwa basu samu daman samun ilimi ba, kuma basu da wata hanyar daukaka gwanintan su a sama. Sai su mutu babu wani tarihi da suka bari a baya. Dan kasar kwarai duka na son ya mutu ya bar wani abin gado ma yayan shi, shi’a manufar duk mai basira da rana domin cimma nasara a rayuwan sa. Lokaci ya kai na barin tarihi, kuma yana da kyau ka zamo mutun da za’a iya tunawa da kai. Shahararrun maza da suka yi tarihi, mayaka ne, dake yaki har mutuwan su. A duk inda kake, ina gyyatan ka zuwa ga website na me makarantar Active School of Languages, bi ma’ana, makarantar Active me koyar da harsuna iri dabban dabban. Kana kuma iya aika wa da tambayoyi da ra’ayoyin ka ta Electronic Mail na offishin me makarantar. Shine, soloda12@yahoo.com ko kuma activeschool@pnet.pl Ka fadada bangon duniyan ka. Dauki mataki guda a rayuwan ka da zai saka cikin littahin masu suna. Ku kara sunan ka cikin sunayen wadanda suka yi suna a rayuwan su. Kada ka yarda a barka a baya. Ka zamo cikin masu basira. Kada ka ji tsoron daukan shawrwarin kwarai. A duk lokacin da kake shakkan daukan wani shawaran kwarai, ka tunkari abokannai masu basira da zasu baka shawara mai amfani. Ka kuma yi la’akari, kada ka yarda kishi ya hanaka daukan matakan kwarai ma rayuwan ka. Duk wanda baya son daukan nauyin abu, to kurayen kasa zasu canye shi. Muna fatar ganin ranar da dimbin jama’a daga wurare dabban dabban zasu ga sakiya ga rayuwan su a makarantar Active School. Yare, shine hanya guda da zaka iya sanin jama’a da al’adun su. Idan baka jin yaren wani, ba zaka iya fahimtar al’adan shi ba. Kana iya koyon tarihin wasu, to amma idan baka jin harshen su da kyau, za’a boye maka asirai da dama. Ka ji yaren su, haka zai san mutanen da kyau. Idan an haife ka gwani, ya kamata ka nuna wa duniya irin abinda zaka iya yi.

Ka zamo daya daga ciki wannan shiri mai tarihin gaske. Kada ka yarda a bar ka a baya. Ka hada kai da wadanda ke bukatan daukaka rayuwan jama’a dake neman ilimi, in wurin aiki ne, a gida ne, ka zamo wanda ba za’a taba mantawa da kai ba. Ka daukaka matsayin ka. Ka daukan ma kanka shwarar irin aikin da kake son kayi a rayuwan ka. Kada ka bari aikin ya daukan maka shwara. Ka zamo mai babban gida, ba mai lease gida ba. Ka tuna fa, idan ka bar wani abu a baya sabili da kiwya, zaka sake dawowa gareshi a wani lokaci, ko kuma ka manta da shi, ka ga laifin kan ka a duk sawon rayuwan ka. Wayannan zantuttukan, bana mai gani kai bane da jahili. Ka zamo wanda za’ayi koyi da shi, ba ka zamo mai koyi da wani ba. Kayi amfani da lokacin ka tun kana da kuruciya. Kada kuma ka ce lokaci ya kure ma rayuwan ka a lokacin da kake da kwarjini, karfi, da lahiya. Killan abu guda da zaka bukaci shine goyon baya. Idan kaje wurin shakatawa kamar wurin shan shayi da wani, kada kayi tunanin cewa, shi mai saye ne Kaman ka. Yana iya zama mai babban kampanin yin mototi, a bayan gidan ka. Kada ka taba cewa lokaci ya kure a rayuwan ka. In kai mugun mutun ne, kana iya mai da wurin ka wurin bautan Allah ko wurin wasan kwallon kafa. Wasu sun yi suna a rayuwan su, kai ma kana iya yin suna, to amma suna mai kyau da za’a iya tunawa da kai. Ka zo Active school, ka koyi wani abu mai amfani da zai kawo sakiya ga rayuwan ka. Ka nuna cewa, kana da ilimi, ka nuna cewa ka san wan abu. Kada ka saura baya. Ka sanar da duniya cewa kai ma wani ne. Kada kuma ka taba tunanin cewa kai kafi kowa sani. Kada ka taba gajiya da neman ilimi. A duk inda kake, kuma a duk inda ka ga kan ka, ka tuna cewa, Makarantar Active, shine wurin ka kuma naka ne.

Wrocław activeschool@activeschool.com.pl , soloda12@yahoo.com tel/fax:341-91-10, tel:341-91-54, mobile:607986645

|Szkoła językowa Wrocław | Język niemiecki Wrocław | Język angielski Wrocław | Język chiński Wrocław |
| Język hiszpański | Język włoski | Język francuski | Język rosyjski | Język szwedzki | Język wietnamski |
| Język fiński | Język japoński | Język niderlandzki | Język portugalski | Język norweski | Język arabski |
| Język turecki | Język hausa | Język grecki | Język chorwacki | Język duński | Język twi |
| Język swahili | Język polski | Język rosyjski | Język koreański | Język łaciny | Język migowy | Język tagalog |
| Język urdu | Język hindi | Język litewski | Język laotański | Język albański | Język bo¶niacki | Język bułgarski |
| Język węgierski | Język rumuński | Język perski Wrocław | Język ukraiński |
| Język słoweński | Język słowacki | Język macedonski | Język hebrajski | angielski | holenderski | flamański | Język flamański | Język holenderski | niederlandzki | norweski | Język hiszpański | hiszpański| chiński | niemiecki | włoski | francuski | szwedzki | Kursy tygodniowe |

web site designed by Nlandu M. Nguayila email:chrisnlandu@yahoo.com