|
Muna
kuma da wulda da ma’aikatan kula da ilimi na kasar Portugal, Italy,
Ecuador, Ghana, Canada, Amurka, Britian, Australia, Brazil, Angola,
Zimbabwe, Togo, Benin, Ivory Coast, France, Switzerland, Holland,
Netherlands, Finland, Denmark, Sweden, Norway, Germany da Belgium.
Yin haka zai taimaka wurin sanin matsayin makarantun su da jami’oin
su, da kuma irin kokarin da ake bukata daga dalibai a kasashen dabban
dabban. Wannan matakin da muka dauka, ya taimaka muna wurin samun
daukaka fiye da na sauran makarantun wasu kasashen dabban. Bayan
kamala karatun daliban mu, yana dora su sama da sauran daliban wasu
makarantun da jami’oin. Muna samun labari ne game da irin tsarin
koyar da karatun su, da kuma irin ababan da suke amfani da su wurin
karatu na semester da na ko wace shekara, irin littafan da suke
amfani da su sa’anan su samu Degree na Masters a jami’oin wayanan
kasashen, da kuma yanda suke tahiyar da tsarin jarabawan su. Muna
kuma samu labari game da dalibin su da yafi duk dalibai kokari.
|